1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brahimi ya gana da 'yan adawar Siriya

September 14, 2012

A ziyararsa ta farko zuwa Damascus manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya domin sulhunta rikicin Siriya Lakhdar Brahimi ya gana da bangaren 'yan adawa

Diplomat Lakhdar Brahimi speaks with former U.S. President Jimmy Carter (not pictured) during a joint news conference in Khartoum in this May 27, 2012 file photo. Veteran Algerian diplomat Brahimi is expected to be named to replace Kofi Annan as the U.N.-Arab League joint special envoy for Syria barring a last-minute change, diplomats said on August 10, 2012. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah/Files (SUDAN - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Manzon musamman na kasa da kasa domin samar da zaman lafiya Siriya Lakhdar Brahimi ya gana da 'yan adawa a sabon yunkurin da yace na wanzar da zaman lafiya. kakakin 'yan adawan Hassan Abdel Azim yace sun baiyanawa jakadan na musamman cewa a shirye suke su bada hadin kai domin kawo karshen hasarar rayuka tare da samar da magunguna wadanda suka jikata da kuma ganin an sako fursunonin siyasa da ake tsare da su. Brahimi wanda ke ziyararsa ta farko a Damascus tun bayan nada shi mai shiga tsakani don kawo karshen rikicin Siriya zai gana da bangorin 'yan adawa da kuma gwamnati inda tuni ya sadu da ministan harkokin wajen Syria Walid Mualem. Ana kuma sa ran zai gana da shugaba Bashar al-Assad a ranar Asabar din nan.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe