Brazil: An baza soji don murkushe zan-zanga
May 25, 2017Gwamnatin Brazil ta dauki matakin baza sojoji a Braziliya babban birnin kasar inda wata zanga-zangar kin jinin gwamnatin Shugaba Michel Temer ke neman rikidewa zuwa tarzoma, bayan da masu zanga-zangar suka fara cinna wa gine-ginen ma'aikataun gwamnatin kasar wuta.
'Yan sandar kasar ta Brazil sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar lokacin da suka yi yinkurin tunkarar fadar shugaban kasar ta Planalto tare da cinna wa ofishin ministan noma na kasar wuta. Lamarin da ya kai gwamnatin ga fiddo sojoji domin taimaka wa 'yan sandar a cikin aikin kwantar da tarzomar.
Mutane 49 suka jikkata a yayin da aka kama wasu guda bakwai a lokacin wannan zanga-zanga da kungiyoyin kwadagon suka kira da nufin tilasta wa Shugaba Michel Temer yin murabus bayan da aka bankado wata badakalar cin hanci da aka same shi da hannunsa dumu-dumu a ciki.