1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lula zai yaki cin hanci da rashawa a Brazil

August 26, 2022

Tsohun shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva wanda ya kwashe watanni 19 a gidan yari bisa laifukan cin hanci ya sha alwashin yakar rashawa a kasar.

Tsohon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva
Hoto: Miguel Schincariol/AFP

Lula ya ce zai kawo sabbin tsare-tsare na binciken cin hanci da rashawa da hukunta duk wanda aka kama da laifin  idan ya lashe zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Oktoba. 

An dai yanke wa tsohun shugaban kasar wanda ya jagoranci Brazil daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2010 hukuncin ne kan laifin cin hanci mafi girma a kasar wanda ya haifar wa gomman 'yan siyasa da 'yan kasuwa fuskantar hukunci, sai dai kuma an wanke shi daga baya wanda hakan ya ba shi damar sake neman tsayawa takara.

Kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a dai na nuni da cewa, Lula na kan gaba akan abokin hamaiyarsa shugaba mai ci Jair Bolsonaro.