Brazil ta yi watsi da barazanar Trump ta kara mata haraji
July 18, 2025
Shugaban kasar Brazil Lula da Silva ya bayyana matakin shugaban Amurka Donald Trump na kara wa kasarsa haraji na kashi 50% a matsayin bita da kulli da shiga sharo ba shanu a game da lamuranta na cikin gida.
Shugaba Lula ya kuma yi gargadi ga wasu 'yan siyasan Brazil da ya bayyana a matsayin ''maciya amanar kasa'' saboda goyon bayan da suka nuna ga wannan barazana ta Trump ta kara haraji ga kasar da ke zama mafi karfin tattalin arziki a yankin Latin Amurka.
A ranar Alhamis a cikin wani sako ta aike wa tsohon shugaban Brazil Jair Bolsonaro wanda yanzu haka ke cikin komar kotu kan zargin kitsa juyin mulki, Donald Trump ya bukaci gwamnatin Lula da ta daina muzgunawa dan siyasan.
Karin bayani: BRICS na tsara tunkarar manufofin shugaban Amurka Trump
A game da wannan mataki na ladabtar da Brazil ta hanyar karin haraji da Trump ke kokarin yi, a Larabar da ta gabata fadar mulki ta Rio da Janeiro ta wallafa wata budaddiyar wasika inda ta ce a shirye take ta tattauna da Amurka don samin masalaha dangane da mu'amalar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.