Shugaba Bolsonaro na Brazil ya yi watsi da dokar Corona
July 4, 2020Talla
Majalisar dokokin kasar dai ta amince da wasu dokoki ne guda biyu wadanda suka tilasta wa jam'a sanya takunkumi a wuraren taruwar jama'a da a shaguna da kuma Coci, da kuma tarar kudi ga wadanda suka ki mutunta su.
Dokokin da Shugaba Bolsonaro ya hau kujerar naki kan amfani da su yana mai cewa sun saba dokar tsarin mulkin kasar wacce ta ke ba da kariya ga siirukan rayuwar dan Adam. Majalisar dokokin kasar ta Brazil dai na da kwanaki 30 domin cilasta amfani da dokokin na Corona ko kuma yin watsi da su.