Yunkurin neman gurfanar da Shugaba Michel Temer
October 17, 2018Ana zargin shugaban kasar ta Brazil Temer tare da wadannan mutane 10 da laifin karbar cin hanci da rashawa, da halasta kudadan haramu. Rundinar 'yan sandan ta Brazil dai ta kaddamar da wani bincike ne sama da shekara guda, domin tantance ko shugaban Temer da ke kan karagar mulkin kasar tun daga shekara ta 2016 na da hannu cikin wata badakala ta cin hanci, inda ake zarginsa da karbar toshiyar baki kafin ya amince da wani kudiri a shekara ta 2017, wanda zai taimaka wa ayyukan wasu kamfanoni na tashoshin ruwa a kasar.
A halin yanzu dai kallo ya koma ga ma'aikatar shari'ar, ko za ta shigar da kara na shugaban kasar, ko za ta nemi a aiwatar da bincike kwakwaf, ko kuma ta yi watsi da batun. Ga kundin tsarin mulkin kasar ta Brazil dai, sai majalisar dokokin ta amince ne kotun kolin kasar za ta iya aiwatar da na ta bincike tare da gurfanar da shugaban kasar.