1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brazil ta yi kashedi kan afkawa Venezuela

Abdullahi Tanko Bala
December 20, 2025

Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula de Silva ya yi kashedin cewa Trump Amurka na afka wa Venezuela da karfin soji zai iya haifar da mummunan tagaiyarar al'umma yayin da Amurka ke zafafa matakai kan Venezuela mai makwabtaka.

Taron shugabannin kasashen kudancin Amurka kan rikicin Venezuela
Taron shugabannin kasashen kudancin Amurka kan rikicin VenezuelaHoto: Evaristo Sa/AFP

A ranar Talata shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin toshe dukkan jiragen dakon mai da ke shiga ko fita daga Venezuela a matakin baya bayan nan na matsin lamba kan gwamnatin Nicolas Maduro don toshe manyan hanyoyin da gwamnatin ke samun kudin shiga.

Lula da shugabar Mexico Claudia Sheinbaum, shugabannin manyan kasashe biyu na kudancin Amurka masu karfin tattalin arziki sun yi kira a kai zuciya nesa a kuma kwantar da hankula.

Sai dai yayin wani taron koli na kasashen kudancin Amurka, Lula ya ja hankali kan abin da ya ce na iya zama babban hadari.

Ya ce fiye da shekaru 40 bayan yakin Falkland tsakanin Argentina da Burtaniya, nahiyar kudancin Amurka na sake fuskantar barazanar soji daga wata babbar kasa ta duniya.