Brazil: Za a tuhumi Bolsonaro da tarzomar zabe
January 14, 2023Kotun kolin Brazil ta sanya tsohon shugaban kasar Jair Bolsonaro cikin mutanen da take tuhuma a game da kutsen ginin Majalisar Dokokin kasar da ke Brasilia da magoya bayan tsohon shugaban suka yi a ranar 8 ga watan Janairu.
Tsohon shugaban na Brazil da ya tsere kasar Amurka gabanin rantsar da sabuwar gwamnati ya musanta hannu a cikin tashe-tashen hankulan da ke faruwa a kasar. Sai dai kuma sabon shugaban kasa Lula da Silva ya dora masa alhakin tarzomar bayan zaben da ke gudana.
Tun gabanin zaben shugaban kasa na shekarar da ta gabata, Bolsonaro, ya fara hasashen za a tabka masa magudi a zaben. Wannan ta sa duk da nasarar da hukumar zaben kasar ta bai wa Lula da Silva, magoya bayan tsohon shugaban da shi kansa suka ki amincewa da sakamakon zaben, lamarin da yanzu ke ci gaba da haifar da tashin hankali.