Brazil za ta bujuro da sauye-sauyen tattalin arzikin kasa
May 24, 2016Talla
A yayin da yake ganawa da manema labarai a kasar Mukaddashin shugaban kasar yayi nuni da cewar a kwai bukatar kawo sauyi mai ma'ana ta fuskar bunkasa tattalin arzikin kasar.
Michel Temer ya kara da cewar:
Kashe kudaden gwamnati barkatai ba za su kai mu ga ko'ina ba, za mu iya dadadawa kan mu to amma ci gaba da yin hakan zai sanya mu jefa al'ummar Brazil cikin wani mawuyacin hali a don haka ya zama wajibi mu dakatar.
Michel Temer wanda ya karbi shugabancin kasar ta Brazil a watan Mayu bayan da aka dakatar da Dilma Rousseff kafin sauraron karar tsige ta daga mulki na yunkurin bunkasa harkokin mulkin kasar da ke fuskantar tarin kalubale kama daga na tattalin arziki da na siyasa.