Brexit: Theresa May na kokarin shawo kan 'yan majalisa
January 28, 2019Talla
Kakakin Firaiministar, ya sanar da cewa, akwai bambanci a tsakanin tsohon shirin da kuma sabon, ya kara da cewa yanzu an shiga sabon babi inda ake sa ran gudanar da wani zabe na raba gardama, sai dai a wannan karon babu wani dalili na kin amincewa 'yan majalisar na yanke dangantaka da EU a cewarsa.
A ranar ashirin da tara ga watan Maris na wannan shekarar ta 2019, Birtaniya ke fatan ganin ta fice baki daya daga Tarayyar Turai sai ana baiyana shakku kan hakan ganin irin tirjiyar da ta fuskanta tun daga farkon shigar da kudirin.