Brexit: Jakadun EU sun tattauna cinikayya
December 25, 2020Talla
Jakadu daga kasashen 27 na kungiyar tarayyar Turai sun gana a yau kirismeti don fara tantance yarjejeniyar cinikayya mara shinge da kungiyar ta kulla da tsohuwar mambarta Birtaniya yarjejeniyar dake zama babban abin tarihi.
A taron na mussaman, wakilan EU sun bukaci karin lokaci don yin nazari kafin turawa ga 'yan majalisar tarayyar Turai kuma ake sa ran jakadun su kara ganawa a ranar Litinin mai zuwa a cewar wani jami'in diflomasiyyar kungiyar.
Firanminsitan Birtaniya Boris Johnson ya yabawa yarjejeniya inda ya baiyanata a matsayin matakin farko na alakar danganta tsakanin Birtaniyar da makwaftanta na tarayyar Turai.
An dai cimma matsayar cewa karkashin yarjejeniyar babu kudin fito ko kayyade cinikayya a tsakanin bangarorin biyu.