Brexit: May za ta sake tattaunawa da shugabannin EU
January 21, 2019Talla
Duk da rashin tasirin Firaministar Birtaniya Theresa May kan daftarin ficewar Birataniya daga EU a majalisar dokokin Birtaniya a makon jiya, amma ta ce ba gudu ba ja da baya kan kudurin ficewar kasar daga EU.
"Da farko akwai alamar yuwar ballewar biratbiya daga kungiyar tarayyar Turai ba tare da wata yarjejeniya ba. Kuma bisa ga dukkan alamu dukkannin bangaorin majalisa na son gwamnati ta cimma wannan mastaya. To amma yakamata mu gayawa kanmu gaskiya mu fayyacewa jama'a a abinda hakan ke nufi. Hanya mafi dacewa na cimma hakan ba tare yarjejeniya ba shi ne majalisa ta amince da yarjejeniya tare da kungiyar EU. Wannan shi ne gwamnati ke fata.