1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaitaccen tarihin sabon firaminista Boris Johnson

Abdourahamane Hassane RGB
July 23, 2019

Boris Johnson da ke goyon bayan ficewar Britaniya daga Kungiyar tarayyar Turai, ya yi nasarar zama Firaministan da zai maye gurbin Theresa May

Großbritannien London | Boris Johnson wird neuer Premierminister
Hoto: Reuters/T. Melville

Mutumin da ake yi wa kallon jagaba na wadanda suka yi ruwa suka yi tsaki kan ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar tarrayar Turai Boris Johson ya samu nasara da gagarumin rinjaye a zaben maye gurbin firaminista Theresa May. Ya ko yi nasara ne a gaban ministan harkokin waje na Birtaniyan Jeremy Hunt. Tsohon magajin garin birnin Landan kuma tsohon ministan harkokin waje na Birtaniya Boris yana da bakin jini a idon wasu 'yan siyasa sai dai kuma jama'a na sonsa. Zaben na wakilan jam'iyyar Conservative 16000 ya aza Boris Johson dan shekaru 55 a matsayin sabon Firaministan a gaban Jeremy Hunt dan shekaru 52.


Ya samu rinjaye da kuri'u dubu casa'in da biyu da dari daya da hamsin da uku a yayin da Jeremy ke da kuri'u dubu arba'in da shida da dari shida da hamsin da biyar. Boris Johson wada aka haifa a New York a shekarar 1964, maifinsa dan majalisar ne kana mahaifiyarsa. Ya fara aikin jarida, a jaridar Times kafin daga bisani ya zama wakilin jaridar Telegraph, jarida ta biyu mafi karfin fada a ji a Birtaniyan bayan jaridar Times. Hakan ya sa yayi suna tare da samun kwarjini a idon jama'a, duk da irin katobarar da yake yawan yi. A farkon shekaru 1990 ya shiga siyasa sai dai kuma ya yi takara a zaben 'yan majalisun dokoki ba tare da samun nasara ba, kafin a shekara ta 2001 ya yi nasara samun zaben kansila a Oxford.

Jeremy Hunt ya taya abokin takararsa Boris Johnson, murna nasara a zabenHoto: picture-alliance/empics/S. Rousseau


Shekaru bakwai dai bayan da ya rike matsayi na siyasa a Oxford a zabe shi a matsayin magajin garin birinin Landan daga nan kuma duniya ta fara sanisa ya yi suna sosai wanda a lokacin ya yi shelar cewar ya kawo sauye-sauye a birnin tare da yin sabin gine-gine kafin daga baya, da jamiyyarsa ta samu nasara a zaben Birtaniya ya zama Minista harkokkin waje a tsohuar gwamnatin Theresa May.
A yanzu dai an zuba idanu don ganin irin ci gaba da za a samu kan takaddamar da ke a tsakanin Birtaniya da kungiyar tarrayar Turai a kan maganar ficewar Birtaniyan daga cikin kungiyar.