British Airways zai biya diyya saboda mazambata
September 7, 2018Talla
Shugaban hukumar gudanarwar kamfanin Alex Cruz ya bayyana batun biyan diyyar a wannan rana ta Juma'a lokacin da yake neman afuwar kamfanin ga masu hulda da kamfanin saboda matsalar da aka samu.
A yammacin Alhamis kamfanin jiragen saman na British Airways ya bayyana cewa bayanai da harkokin kudade na masu hulda da kamfanin su 380,000 da suka sayi tikiti ta hanyar shafin Intanet ko manhajar kamfanin tun daga ranar 21 ga watan Agusta zuwa ranar Laraba an sace su.
Wannan dai na zuwa ne watanni bayan da Kungiyar Tarayyar Turai ta tsaurara dokoki na kare bayanan al'umma karkashin dokar kare bayanai ta (GDPR).