1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buƙatar agaji ga al'ummar Siriya

February 15, 2012

Turkiyya ta nemi Majalisar Ɗinkin Duniya ta tsoma baki wajen kaiwa 'yan Siriya taimako

epa02826121 Turkish Foreign Minister Ahmet Davutoglu speaks during a press conference as she attended with US Secretary of State Hillary Clinton (not pictured) in Istanbul, Turkey on 16 July 2011. Clinton is in Turkey for two days visit. EPA/TOLGA BOZOGLU +++(c) dpa - Bildfunk+++ usage Germany only, Verwendung nur in Deutschland
Ahmet Davutoglu, ministan wajen TurkiyyaHoto: picture alliance/dpa

Ƙasar Turkiyya ta buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga shugabannin Siriya su bayar da damar kai agaji ga 'yan ƙasar dake fama matsala sakamakon watannin da aka yi ana zubar da jini a ƙasar. A lokacin daya ke magana da manema labarai, ministan kula da harkokin wajen Turkiyya Ahmet Davutoglu ya ce kamata ya yi Majalisar Ɗinkin Duniya ta shiga tsakani, ba wai kawai ga batutuwan da suka shafi siyasa ba, a'a harma da abubuwan da suka shafi jin ƙan bil'Adama, yana mai alƙawarin cewar, Turkiyya za ta ci gaba da gabatar da rikicin Siriya cikin batutuwan da Majalisar Ɗinkin Duniyar za ta tatttauna.

Turkiyya wadda a da ke da kyakkyawar dangantaka da Siriya gabannin katse hulɗar dai, a yanzu tana sahun farko tare da ƙungiyar Larabawa da wasu ƙasashen yammacin duniya wajen neman kawar da mulkin shugaba Assad na Siriya sakamakon matakan gallazawar da gwamnatin sa ke ɗauka akan masu zanga-zangar neman sauyi.

A halin da ake ciki kuma, babban sakataren ƙungiyar ƙasashen Larabawa Nabil al-Arabiy, wanda ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin fadar gwamnatin ƙasar, ya ce nauyi ne dake kan ƙungiyar tabbatar da kawo ƙarshen rikicin Siriya:

" Ya ce abinda yake faruwa a Siriya a yanzu, abu ne daya dace mu ƙasashen Larabawa mu kawo ƙarshen sa. Tilas ne mu ga cewar an dakatar kissar da ake yi a ƙasar."

A wani ci gaban kuma, a yayin da ƙungiyar Larabawar ke shirin gabatar da wani sabon ƙudiri akan rikicin Siriya ga kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya bayan da ƙasashen Rasha da China sun hau kujerar naƙi ga ƙudirin da ta gabatar a can baya, ministan kula da harkokin wajen Rasha ya ce zai gana tare da takwaran aikin sa na Faransa a birnin Vienna domin tattauna batun rkicin na Siriya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu