Buƙatar Siriya ga Majalisar Ɗinkin Duniya
September 2, 2013Siriya ta buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya da ta yi ƙoƙari ta daƙile duk wani matakin da zai janyo ƙarin tashin hankali a Siriya. Kamfanin dillancin labaran ƙasar na SANA ne ya rawaito hakan a daidai lokacin da Amirka ke tattauna yiwuwar ɗaukar matakin soji kan Damascus.
Gwamnatin Siriyar ta miƙa wannan buƙate ne a wata wasiƙa da ta tura majalisar, tana buƙatarta taimaka wajen samar da sulhu a siyasance ga rikicin ƙasar wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
A halin da ake ciki dai Shugaba Barack Obama na Amirka, neman amincewar majalisar dokokin ƙasar wajen ɗaukar matakin sojik, domin mayar da martani kan zargin amfani da makamai masu guba, waɗanda suka kai ga hallakar ɗaruruwan mutane.
Yawancin gwamnatocin ƙasashen yamma da suka haɗa da Birtaniya da Faransa da Amirka na zargin gwamnatin Siriyar da aikata wannan ta'asa, duk da cewa Damascus ta ƙaryata wannan zargi.
Daga farkon wannan shekarar Amirka da Rasha suka amince su aiki tari wajen gudanar da wani taron ƙoli a Geneva dan sassanta rikicin sai dai sannu a hankali wannan matakin na fuskantar barazanar gushewa.
A wani labarin kuma, ƙasar Iran ta faɗawa Majalisar Ɗinkin Duniya cewa a shirye take ta samar da maslaha ga rikicin Siriyar cikin kwanciyar hankali. Ministan harkokin wajen ƙasar Mohammed Javad Zarif ne ya bayyana hakan, ga babban sakataren majalisar Ɗinkin Duniyar Ban Ki-Moon.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Awal Balarabe