1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buƙatar taron duniya akan Siriya

February 8, 2012

Turkiyya ta bayyana ƙudirin shirya taron neman mafita ga rikicin Siriya

AUSSCHNITT Syrian President Bashar Assad, left, and his wife Asma Assad, listen to explanations as they visit a technology plant Tuesday July, 13, 2010 in Tunis. President Assad is on a two-day visit to Tunisia. (AP Photo/Hassene Dridi) *** Turkey's Prime Minister Recep Tayyip Erdogan announces his new cabinet during a press conference in Ankara, Turkey, Wednesday, July 6, 2011. Erdogan said his new government includes a new minister to oversee Turkey's European Union membership bid. Erdogan named Egemen Bagis, the country's chief EU negotiator, as the minister for EU affairs. Ahmet Davutoglu remains the Foreign Minister.(AP Photo/Burhan Ozbilici)
Shugaba Assad da firaminista ErdoganHoto: AP/Montage:DW

Ministan kula da harkokin wajen Turkiyya Ahmet Davutoglu ya shaidawa kamfanin dillancin Labarai na Reuters cewar a shirye ƙasar sa ta ke ta karɓi taron ƙasashen duniya da nufin tallafawa al'ummar Siriya, kana da aikewa da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na ƙasar da saƙon dake cewar, tilas ne ya kawo ƙarshen gallazawar daya kwashe tsawon watanni 11 yana yiwa 'yan adawa.

Davutoglu, wanda ke shirin zuwa ƙasar Amirka domin tattaunawa akan batun Siriya, ya ƙara da cewar tarihi ya nuna cewar dukkan shugabannin dake kissar al'ummomin su ba su rayuwa na lokaci mai tsawo ba. Ya ce idan har kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya gaza bada kariya ga fararen hular dake Siriya, to, kuwa kamata yayi ƙasashen dake da dattaku su ɓullo da hanyoyin kawo ƙarshen kissar da ake yiwa jama'a da kuma samun damar kai agaji ga fararen hular da dakarun soji suka yiwa ƙawanya a birnin Homs.

Ministan harkokin wajen na Turkiyya, ya ce babu ko shakka suna hanƙoron shirya taron ƙasa da ƙasa da zai tattauna halin da ake ciki a Siriya, wanda ko dai ita Turkiyya ce za ta karɓi baƙuncin sa ko kuma wata ƙasa ta daban.

Tunda farko dai firaministan Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana buƙatar sake wani yunƙurin samar da mafita ga Siriya:

" Ya ce muna buƙatar shata sabuwar alƙibla game da matsalar Siriya, wadda za ta tattara dukkan ƙasashe wuri guda, wadda kuma ba kawai za ta taimakawa gwamnati ba, a'a harma da al'umma."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou