1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buɗe kan iyakokin Masar da Falasɗinu

May 28, 2011

Falasdinawa sun fara shige da fice tsakaninsu da ƙasar Masar

Kan Iyakar Gaza da FalasɗinuHoto: picture alliance / landov

Ƙasar Masar ta buɗe kan iyakokin ta da Falasdinu bayan da aka shafe fiye da shekaru biyar ana fama da kangin takunkumin hana shige da fici. Yanzu haka dai Falasɗinawa a zirin Gaza sun fara kai komo a tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaban hukumar shige da fice ta Falasɗinu Hatim Uwaidha ya ce wannan wata nasara ce "wannan mataki da ƙasar Masar ta ɗauka na nuna kyaukyawan alaƙar da ke a kwai tsakanin mu da su. Kuma wannan yunƙuri na Hukumomin ƙasar ta Masar na zaman canji da aka samu tun bayan juyin juya halin da ya kawar da shugaba Hosni Mubarak wanda a lokacin sa 'yan ƙasar Masar din da ma sauran larabawa ke cike da fushi saboda abinda suka kira haɗa baki da tsofon shugaban ya ke yi da Isra'ila Wajen killace Falasɗiniwan Gaza waɗanda addadin su ya zarta miliyan biyu".

Motocin jigila na fasinja da motocin daukar marasa lafiya cike da jamaa makil sun riƙa wuce shingen da ya killaci al'ummar Gaza zuwa ƙasar Masar

walau ganin yan uwa ko kuma neman magani.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Abdullahi Tanko Bala