Sake jigilar matafiya jirgin sama a Hong Kong
August 14, 2019Talla
An sake bude filin jirgin sama a HongKong da sanyin safiyar wannan Laraba sa'o'i bayan dakatar tashin jiragen sama a filin jirgin bisa kazancewar zanga-zangar neman sauyi a Hong Kong da ta bazu zuwa harabar filin.
Sai dai sake buda filin jirgin na zuwa a daidai lokacin da kasar China ta zargi cin zarafin 'yan kasarta biyu a yankin na Hong Kong, sakamakon likida masu kashi da masu zanga-zangar suka yi, lamarin da kuma kasar ta kira da ta'addanci.