1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Amurka za ta bude iyakokinta Mexko da Kanada

Abdoulaye Mamane Amadou
October 13, 2021

Watanni 19 bayan da Amurka ta rufe iyakokinta da Kanada da Mexiko don yaki da annobar corona, gwamnatin kasar ta sake sanar da bude kofofinta ga wadanda suka yi allurar rigakafin corona.

Grenzübergang USA Kanada - Flüchtlinge
Hoto: Getty Images/AFP/D. Emmert

Amurka za ta sake bude iyakokinta na kasa ga kasashen Mexiko da Kanada ga wadanda aka yi wa alluran rigakafin corona daga farkon watan gobe. Wani kusa a fadar White House ne ya bayyana haka a wannan Laraba, a ci gaba da sakin mara wa tsauraran matakan kariya da annobar corona da ta yi mumunan illa ga kasar.

Tun a cikin watan Satumban da ya gabata, gwamnatin Amurka ta ambaci shirin bude iyakokinta na sama ga wasu kasashen nahiyar Turai da Birtaniya ga suka yi alluran rigakafin cutar shekara daya da rabi bayan da kasar ta takaita shigar 'yan kasashen karkashin gwamnatin tsohon shugaba Donald Trump.