Bude taron sauyin yanayi a Nairobin,Kenya
November 6, 2006An bude taron sauyin yanayi wanda zai mayar da hankali wajen tallafawa kasashe matalauta,akarkashin jsagorancin mdd a Kenya.Wakilai daga sassa daban daban na duniya ke halartan taron,wanda ke zama irinsa na farko da aka gudanar a wata kasar Afrika dake kudu da sahara.A jajibirin wannan taro,dai mdd ta fitar da wani rahoto adangane da batutuwa da zaa tattauna,dangane da sauyin yanayi a wasu yankunan Afrika.Inda zaa samu koma baya a albarkatun gonaki,ayayinda tekuna zasu yi ambaliya zuwa cikin birane.Wannan taron na birnin Nairobi,wanda ke zama na 12 irinsa a karkashin jagorancin mdd,tun bayan rattaba hannu a yarjejeniyar sauyin yanayi a 1992,sai dai a makon daya gabata ne aka fitar da wani rahoto dake bayyana karuwar hayakin gas dake haddasa dumamar yanayi.