1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Buhari karo na farko a Yobe?

January 9, 2023

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki a karo na farko a jihar Yobe, inda ya kaddamar da wasu ayyuka da su ka shafi inganta tsaro da kuma farfado da harkokin rayuwa da tattalin arzikin kasa.

Najeriya | Muhammadu Buhari | Ziyara | Yobe
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Ubale Musa/DW

Duk da fargabar tsaro da ake ciki a yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar, al'ummar jihar Yobe sun yi cincirindo domin tarbar shugaban kasar Muhammadu Buhari. Da dama daga cikin al'ummar wannan jiha da ke fama da tarin matsaloli dai, ba su taba yin tozali da shugaban kasar ba sai a wannan karo a tsawon shekaru kusan takwas  da ya kwashe yana mulki. Shugaba Buharin dai ya isa Damaturu babban birnin jihar ta Yobe daga Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa, inda ya sauka da tawagarsa a sabon filin jirgin saman jigilar kayayyaki na kasa da kasa. A nan ne kuma ya fara aikin kaddamar da ayyuka, tare da tallafin wasu gwamnoni da shugaban majalisar dattawa gami da 'yan majalisu na kasa.

Jihar Yobe na daya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren 'yan ta'addaHoto: Nigerian Television Authority/dapd

A dukkanin wuraren da aka je dai Shugaba Buhari bai yi jawabi ba in ban da a fadar sarkin Damaturu, sai dai kaddamar da ayyukan da aka yi a bangaren jami'an tsaro na 'yan sanda da kuma wanda gwamnatin jihar Yobe ta gudanar da suka hada manyan kasuwanni na zamani da kuma cibiyoyin lafiya gami da manyan makarantu da gidaje masu saukin kuidi domin talakawa da 'yan gudun hijira. Daya daga cikin wurare da aka kaddamar shi ne babban filin jirgin sama na jigilar kaya na kasa da kasa, wanda gwamnatin ta ce zai taimakawa jami'an tsaro wajen ayyukansu. An shirya Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabi a wajen taron liyafa da za a gudanar da daren Litinin a fadar gwamnatin jihar, inda ake sa ran jin muhimman bayanai kan tsaro da tattalin arzikin kasa a yankin Arewa maso Gabas din.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani