Buhari: Muna jinjina wa China kan tallafi
April 12, 2016![Muhammadu Buhari Präsident Nigeria Porträt G7 Gipfel 2015 Schloss Elmau](https://static.dw.com/image/18559508_800.webp)
Talla
Xi Jinping ya ce shekara ta 2016 na kasancewa shekaru 45 cif da kulla dangantakar diplomasiya tsakanin China da Najeriya, kuma dukkanin kasashen sun ribaci dangantaka mai gwabi a tsakaninsu a bangarori da dama.
Kazalika Shugaban kasar China ya ce a shirye suke su kara kulla danganta da Najeriya a fannonin Ayyukan noma, kifi, matatun man fetur,da ma'adanan karkashin kasa gami da bunkasa harkokin masana'antu.
Ana sa bangaren Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa China a bisa irin tallafin da kasar take baiwa Najeriya wajen habaka harkokin ci gaba.
Dukkanin shugabanin biyu sun rattaba hannu a kan wasu yarjeniyoyi masu dama ciki har da noma da sanya hannayen jari.