1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya ce corona na yaduwa a Najeriya

Mouhamadou Awal Balarabe
December 22, 2020

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga jama'a da su yi taka tsantsan dangane da hadarin kamuwa da annobar corona, a daidai lokacin da ake shirin gudanar da bukukuwan karshen shekara.

Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Song

.A cikin wata sanarwa da ya fitar bayan ganawarsa da wani kwamiti na musamman da ya kafa don yaki da covid-19, Shugaba Buhari na Najeriya ya ce a ana samun karuwar wadanda suka kamu da cutar a fadin kasar. Dama tun a yammacin jiya Litinin jita-jitar rufe wuraren taron jama'a da gidajen cin abinci suka watsu a wasu sassa na Najeriya, bayan da kwamiti da ke kula da yaki da corona ya fitar da shawarwari kan yadda za a dakile yaduwar kwayar cutar.

Idan za a iya tunawa dai, a watan Afrilun da ya gabata, gwamnatin tarayya Najeriya ta kafa dokar kulle na tsawan makonni biyar, duk da cewa akasarin 'yan kasar sun dogara kan sana'o'in yau da kullum wajen samun kudin shiga. Cutar ta Corona ta karu matuka a cikin makonni biyu da suka gabata a Lagos da ke zama cibiyar kasuwancin Najeriya, da Abuja babban birnin kasar da kuma Kaduna da ke arewacin kasar.