1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari: Sauya kasafin kudi bai mana dadi ba

Zulaiha Abubakar
June 20, 2018

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana damuwarsa game da yadda 'yan majalisar dokokin kasar suka janye wasu aiyyukan da ya sanya kana suka sanya nasu aiyyukan a kasafin kudin shekara ta 2018.

Muhammadu Buhari Nigeria
Muhammadu Buhari NigeriaHoto: AP

Shugaban na Najeriya ya ambata hakan ne dazu bayan da ya sanya hannu kan kasafin kudin da majalisa ta amince da shi. Tun bayan hawansa mulki, an yi ta samun tinja-tinja tsakaninsa da 'yan majalisar a kan kasafin kudi da kuma wasu kudirorin na ciyar da kasar gaba daidai lokacin da al'ummar kasar ke bayyana damuwar su game da irin jan kafar da ake samu daga bangarorin biyu a kan ayyukan raya kasa.