Buhari ya gana da shugabannin majalisu
March 16, 2018Taron ya dauki lokaci ana sa in sa, sai dai an cimma matakai tsakanin shugaban kasa da ya sa kafa ya shure muradun 'yan majalisun. Rikicin ya faro ne bayan bukatar majalisar dattawa na maye gurbin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta EFCC Ibrahim Magu bukatar kuma da shugaban kasar ya ce ba hali.
Ko bayan nan dai Buhari ya yi watsi da dokokin rundunar zaman lafiya ta Peace Corps da dokar zabe ta shekara ta 2018 da majalisun kasar suka amince. Wannan ya sa 'yan majalisun suka tsaida aikin tantance jami'ai na gwamnatin dama manta da batun kasafin kudin kasar.
Duk da cewar an kai ga gudanar da taron a cikin sirri daga dukkan alamu an kai ga fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Senator Bukola saraki ya ce "Taron yayi tasiri, saboda munsamu damar ba da tamu guddumuwa a kan batutuwanda taron ya maida hankali."
Gwamnatin kasar ta umarci ma'aikatu da hukumomin gwamnati da su koma majalisun kasar domin ci gaba da aikin kasafin kudi.