Buhari ya karbi 'yan makarantar Dapchi 104
March 23, 2018
Cikin tsallen murna da kuma barazana shugaban tarrayar Najeriya Muhammad Buhari ya karbi ‘yan mata ‘yan marantar Dapchi sama da 100 da kungiyar Boko ta Haram ta sako a cikin tsakiyar wannan mako.
Fatima Bashir daya daga cikin ‘yan mata ‘yan makarantar Dapchi ta nuna godiya ga gwamnatin tarrayar Najeriya a wani bikin hada fuskokin ‘yan matan da shugaban kasa dama manyan jami’an gwamnatin tarrayar Najeriyar a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja.
Yara 105 ne dai shugaban hukumar tsaron farin kayan DSS Lawal Musa Daura ya tabbatar da ceto su cikin wani tsari da gwamnatin tace ya kunshi tattaunawa da gindaya sharuda amma babu biyan fansa ko sakin fursunoni.
Duk da tsallen murna da farin cikin shugaban kasar da ya dauki hotuna da ‘yan matan sannan ya basu tabbacin ci gaba da karatunsu, daga dukkan alamu har yanzu hankula basu kwanta ba game da makomar ‘yan matan dama iliminsu a wani abun da ke iya sauya makomar karatun Boko a yankin.
Akalla yara biyu sun kauracewa tozali da shugaban a fadar majiyoyi bayan dagewa ta mahaifinsu dake cewar an kai karshe ga kokarin komawa makarantar Boko a nasu bangaren.
To sai dai kuma a cewa Hon Goni Bukar dan majalisar wakilan tarrayar Najeriyar dake wakiltar al’ummar Dapchin zasu yi kokarin lallami da nufin kwantar da hankulan iyayen yaran.
Sai dai ko ya take iya kayawa a tsakanin talakawa da wakilansu a kokari na komawa makaranta, a nata bangaren ita ma shugabar makarantar Dapchin Kande Abdulkareem ta ce muhimmancin ilimin ne zai kai ga tabbatar da gyaruwar lamura cikin makarantar.
Abun jira a gani dai na zaman kokarin gano ragowar ‘yan matan dama daruruwan mutanen da har yanzu ke cikin ikon kungiyar Boko Haram.