1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Bukatar adalci ga Fulani makiyaya-Amnesty

Uwais Abubakar Idris
January 25, 2024

Kungiyar kare hakin jama'a Amnesty International ta nuna damuwa tare da jawo hankali a kan gaza yin adalci ga ‘yan uwan mutanen da suka mutu a harin da sojoji suka kai yankin Doma da ke jihar Nasarawa

Bafulani makiyayi
Hoto: STEPS

 A ranar 24 ga watan janairun 2023 ne sojojin saman Najeriya suka kai mumunan hari a kan Fulani makiyaya ta hanyar amfanin da jirgi mara matuki. Harin da aka bayyana a matsayin kuskure wanda ya kashe Fulani makiyaya su 40 tare da shanunsu. Shekara guda Kenan da wannan hari amma har yanzu ba'a yi wa ‘yan uwan mutanen da aka kashe adalci ba kamar yadda shugaban kungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty International a Najeriya Mallam Isa Sanusi ya nunar. 

Karin Bayani: Najeriya: Martani kan kisan Fulani makiyaya

Kodayake hediwatar tsaron Najeriya ta gana da wakilan Fulani a Najeriyar a wancan lokaci inda ta yi masu alkawari za ta bincika. Ko ya zuwa yanzu wane mataki aka dauka a kan batu? Alhaji Baba Usman Ngelzarma shi ne shugaban kungiyar Miyyeti Allah Macban wanda ya jagoranci wakilan Fulani a wancan lokaci.

Karin Bayani:Rikicin Fulani da Makomar kiwo a Najeriya

Jinkirin yin adalci ga wanda aka yi wa ba daidai ba babban kalubale ne a cewar Barrister Mainasa Umar masani a harkar shari'a.

Kungiyar ta Amnesty International na jan hakali kauce wa hadarin da ke tattare da yin watsi da lamarin.

Hedikwatar tsaro ta sojojin Najeriya dai ta ki cewa uffan a kan batun, inda ta ce har yanzu ana gudanar da bincike.