Aiwatar da yarjejeniyar sulhu a Mali
May 2, 2016 A yayin da suka fara ziyarar tasu a wasu kasashen yammacin Afirka, ministan harkokin kasashen ketare na Jamus din Frank-Walter Steinmeier da takwaransa na kasar Faransa Jean-Marc Ayrault, sun ya da zango a kasar Mali, inda suka gana da mahukuntan kasar, tare da bukatar su da su tabbatar da ganin an aiwatar da tanade-tanaden yarjejeniyar sulhun da suka cimma da bangarorin tawayen kasar. Ministocin kasashen ketaren na Jamus da Faransa sun kuma kai ziyara sansanin shirin bayar da horo kan yaki da ta'addanci da kuma tsageru na kasashen kungiyar EU da ke Malin. Daga bisani Steinmeier zai ziyarci dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke garin Gao na Arewacin kasar, wanda ke da hadarin rashin tsaro. A duka wadandanan shirye-shirye na tsaro dai, akwai dakarun Jamus da na Faransa da ke bayar da tasu gudunmawar wajen wanzar da tsaro da zaman lafiya a Mali. Da ya ke ganawa da manema labarai jim kadan bayan saukarsu a Malin Steinmeier cewa ya yi:
"Kasancewar ministocin kasashen Turai biyu sun shirya wannan tafiya ba karamin abu ba ne. Wannan na nuni da cewa mun damu da halin rashin tsaro da ake fama da shi a nan da ma nuni da irin goyon bayan da muke da shi ga harkokin siyasar kasar Mali."
A wannan yammacin Litinin din nan biyu ga wannan wata na Mayu ne dai, ake sa ran Steinmeier da kuma Ayrault za su dunguma zuwa Jamhuriyar Nijar inda za su isa cikin dare.