Bukatar dakile samun kudin 'yan ta'adda
February 27, 2015Talla
Wata cibiya da ke Paris kasar Faransa mai yaki da hanyoyin da 'yan ta'adda ke samun kudi, ta fidda sanawar cewa, duniya na bukatar aiki tukuru, domin dakile hanyar da kungiyar IS ke samun kudin ta. A rahoton da kungiyar ta fitar yau Jumama'a, ta bukaci gwamnatocin kasashe su bada himma don katse hanyoyin da kugiyoyin ke samun kudin shiga. Rahoton yace akasarin hanyyoyin da kungiyar ke samun kudi, sun hada da fasa bankuna, da kwasar ajiya da aka yi a rumbuna, da sayar da danyen mai, da kuma karban kudin fansa a mutanen da suke sacewa. A cewar wannan cibiyar, harin jiragen sama da Amirka ke kai wa 'yan IS da kuma faduwar fashin mai a kasuwannin duniya, sun yi mummunan lahani ga kungiyar.