Bukatar isar da agajin gagawa a Sudan
August 24, 2024A watan da ya gabata ne wasu kwararu na kasa da kasa suka yi gargadin cewa sama da rabin al'ummar Sudan miliyan 25.6 za su fada a matsanancin hali na yunwa musamman wadanda ke a manyan sansanonin da ke yankin Dafur, da tuni cutar kwalara ta barke a tsakaninsu.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci masu yaki da juna a kasar da su bada damar shigar da maotoci dauke da kayayakin agaji ga mabukata cikin gagawa.
Wannan bayanin na kunshe ne a wata sanarwar da suka fidda a jiya Juma'a bayan kammala wani zama da ya gudana a birnin Geneva na kasar Switzerland a kokarin kawo karshen rikicin da dakarun gwamnati da na rundunar sa kai ta RSF a Sudan din suka kwashe sama da watannin 16 suna gwabza kazamin fada.
A cewar masu shiga tsakanin wannan rikicin, kokarin sasanta bangarorin Sudan da ke gaba da juna ya ci tura.