Sudan: Mika mulki ga gwamnatin riko
November 4, 2021Talla
Sakatare janar na Majalisar ta Dinkin Duniya Antonio Guterres ya kuma bukaci jagororin juyin mulkin na Sudan, su tsara hanyoyin kafa gwamnatin rikon kwarya. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin sakataren na Majaliasar Dinkin Duniya ya fitar, inda ya ce Guterres din ya kuma yi kira ga sojojin su sako Firaminista Abdalla Hamdok da sauran fararen hular da jagororin juyin mulkin ke tsare da su.