1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ECOWAS: Bukatar sababbin tsare-tsare

April 17, 2024

Masana da kwararru na nazarin cewa kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, na bukatar sake tsari da sauye-sauyen da za su yi daidai da manufofin kasashe mambobinta.

Najeriya | Abuja | ECOWAS | CEDEAO | Nijar | Mali | Senegal | Burkina Faso
Bukatar sake tsari da kawo sababbin sauye-sauye a kungiyar ECOWAS ko CEDEAOHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Wannan nazari ne dai na zuwa ne, bayan gaza katabus wajen daukar mataki a kan sojojin da suka yi juyin mulki a wasu kasashen kungiyar da ake ganin ECOWAS din ko CEDEAO ta yi. Ga misali sabon shugaban kasar Senegal na da kusan manufofi daya da kasahen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar da suka fice daga ECOWAS din ko CEDEAO din, tare da kafa wata kungiya ta kasashen yankin Sahel da suka yi wa lakabi da AES. Shin yaya zaman kasar ta Senegal, zai kasance a cikin ECOWAS da ma makomar kungiyar? An dade ana daukar kungiyar ta ECOWAS din ko CEDEAO, a matsayin kungiyar da ta fi ci-gaba a Afirka. Sai dai yanzu abun ba haka yake ba, domin juyin mulkin da sojoji suka yi a kasashe dabam-dabam na yankin ya nuna cewa kungiyar ba ta da hurumi ko karfin na fada a ji wajen magance matsalolin yankin.

Karin bayani: ECOWAS za ta karfafa dimukuradiyyarta

Ya zama wajibi idan kungiyar tana son samun galaba ta nuna kishin Afrika, ta haka ne kadai za ta iya samun amannar kasashen yankin. To sai dai, tana da rauni a kan hakan. Tun farko kungiyar ta ECOWEAS ta yi wa kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso musamman ma dai Nijar barazanar kai hari, idan ba a mayar da Shugaba Mohammed Bazoum kan mulki ba. Kwararu na cewar wannan shi ne kuskure na farko da kungiyar ta yi, kafin ta yi na biyu ta sakawa Nijar din takunkumin da dawo ta cire shi da kanta. Daraja ta fadi karfi ya zama yawa sai ya zamanto an kai ga dole kanwar naki, ECOWAS din ke rarrashin kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Fason, saboda ficewar da suka yi daga cikin kungiyar tare da kafa kungiyar AES ta kasahen yankin Sahel a kan sababbin manufofi na nuna adawa ga kasashen yammacin duniya saboda abin da suka kira katsa-landan da suke yi musu.

Sabon zababben shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye FayeHoto: John Wessels/AFP

A baya ana ganin tamkar shugabannin Nijar da Mali da Burkina Faso na da manufofin neman sauyin hulda da Kasashen Yamma domin sojoji ke mulki, amma sai aka wayi gari wani sabon shugaban kasa na farar hula Bassirou Diomaye Faye da aka zaba a watan Maris a kasar Senegal ya nuna kyama ga tsari irin na mulkin mallaka wanda yake tunanin akwai bukatar a sake lalawa a yi nazari a kan abubuwa da yawa. Faye na ganin akwai bukatar a yi bincike ko kudin yankin CFA Franc wanda ya samo asali tun lokacin mulkin mallaka na Faransa, in yana da alaka da kudin Euro ya kamata a sokeshi. Haka kuma yana son sake tattaunawa kan kwangilolin kamun kifi da kungiyar Tarayyar Turai EU, tare da yin nazari sosai kan kwangiloli da kamfanonin Turai da ke son yin amfani da dimbin iskar gas a gabar tekun Senegal. Da yake jawabi, Shugaba Faye ya ce ya kamata abokan hulda na ECOWAS da yawa su yi koyi da Senegal. In har aka yi la'akari da wadannan maganganu dole ne abubuwa da yawa su canza a ECOWAS, in ji wani manazarcin siyasar Nijar Dicko Abdourahamane.

Karin bayani: ECOWAS: Neman mafita ga rikicin siyasar Senegal

Ana dai ganin shugaban na Senegal yana da kusancin ra'ayi da kasahen Nijar da Mali da Burkina Faso kuma fahimtarsa ​​ga gwamnatocin mulkin soja na kasashen uku ka iya sa shi yin kira da babbar murya ga samun sauye-sauye a kungiyar ECOWAS, domin sake dawo da kasashen na AES cikinta tare da sake tunanin kungiyar na yin kar da kar a gaban kasashen yammacin duniyar ta yadda kungiyar za ta sake samun martaba da darajar a idon dnuinya da ma fada a ji. Carlos Pereira masanin kimiyyar siyasa na kasar  Guinea ya ce hakan na iya yiwa. Jinkiri da sakaci na kin yin hobbasa daga bangaren kungiyar ta ECOWAS wajen ciyar da yankin yammacin Afirka gaba, na daga cikin dalilan faduwar zubewar martabarta. Ana dai ganin tsakankanin kaksashen, wasu na tufka wasu kuma na warware masu ra'ayin tafiyar da ita. Masana na ganin da ba dan haka ba, to da tuni kungiyar ta samar da kudin ECO a matsayin kudin bai daya na yanki yammacin Afirkan.