1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar tallafin Jamus a kan tsaro

Usman Shehu Usman
October 31, 2023

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya yi Jamus ta kawo tallafin yayin da yake ganawa da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz wanda ke ziyara a kasar ta Ghana

Nigeria | Bundeskanzler Olaf Scholz in Abuja
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Akufo-Addo ya ce ayyukan ta'addanci na zama babbar barazana a Yammacin Afirka, inda 'yan jihadi suka bazu a yankin Sahel baki daya. Shugaban kasar ta Ghana ya kara da cewa, a baya kasar Mali ce kawai ake da 'yan ta'adda mafi karfi, amma yanzu sannu a hankali ayyukan ta'addanci na neman zama babbar barazana a Yammacin Afirka baki daya. Ya kuma kwantanta kasar Jamus a matsayin babbar kawa a fannin tsaro, don haka Akufo-Addo yace yana fatan Jamus za ta bada tallafin kayan soja musamman a bangaren leken asiri. Kasar Ghana dai ita ce ta karshe a ziyarar kwanaki uku da shugaban gwamnatin Jamus ya kai Yammacin Afirka, inda ya fara da Tarayyar Najeriya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW