Bukatar tattaunawa da ƙasar Iran
February 9, 2013 Rukunin ƙasashe guda biyar da Jamus waɗanda komitin tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ya ɗora wa alhakin shiga tsakani a rikicin Nukiliyar ƙasar Iran, sun ce a shirye suke su sake tattaunawa da hukumomin ƙIran muddun ƙasar ta amince da sharuɗɗan wata tattaunawar tsakani da Allah inji sakataren harakokin wajen Amirka John Kerry.
Ƙasashen da ke shiga tsakani sun haɗa da Amirka da Birtaniya da Fransa da China da Rasha sannan da ƙasar Jamus marassa zaunanniyar kujera a komitin sulhun. Masu shiga tsakanin dai sun sha kai ruwa rana da hukumomin ƙasar ta Iran a dangane da shirinta na Nukiliya, wanda Iran ɗin ta ce na samar da makamashi ne a maimakon yadda ake zato, yayinda sauran ƙasashen Duniya suka yi amanar cewa ƙasar na shirye shiryen haɗa sindaran da zasu bata damar sarrafa makaman ƙare dangi ne.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Zainab Mohamed Abubakar