Bukatar zagaye na biyu a zaben Senegal
March 2, 2012To madallah. Mafi yawan jaridun na Jamus a wannan mako sun maida hankalin su ne kan al'amura masu daukar hankali a nahiyar Afrika da suka hada har da zaben shugaban kasa a Senegal, inda aka ga alamun cewar sai an kai ga zagaye na biyu tsakanin shugaba Abdoulaye Wade da abokin taiarar sa, ko kuma matakin da jam'iyar ANC dake mulki a Afirka ta kudu ta dauka na koran shugaban reshen matasa na jam'iyar Julius Malema, wanda aka dade ana takaddama kansa saboda aiyukan sa na bata mata suna, sai kuma kasar Somalia, inda batun zaman lafiya ya gagara, duk kuwa da taron da kasashe suka gudanar a London na neman binciko hanyoyin warware halin yaki da kasar take ciki.
Jaridar Süddeutsche Zeitung tayi sharhi a game da zaben shugaban kasa a Senegal, inda tace wannan zabe ya sabawa al'ada a nahiyar Afirka, inda a duk lokacin da aka zo zabe sai an zub da jini. A Senegal ko da shike an ga alamun tilas a kai ga zagaye na biyu na zaben, amma akalla ba'a sami kashe-kashe ba. Duk da adawa mai yawa, amma Abdoulaye Wade, dan shekaru 85 da haihuwa ya tsaya kai da fata sai ya sake wa'adi na uku, duk da cewar kundin tsarin mulkin kasar ta Senegal bai yarda da haka ba. Mai adawa dashi, Macky Sall, shekarun sa 50 ne kawai da haihuwa, kuma da alama shi al'ummar kasar, musamman yan adawa da matasa suka fi son ganin ya kama mulki. Duk da haka, inji jaridar Süddeutsche Zeitung, Wade ya tara manema labarai inda yace shine kan gaba bayan kidaya kuri'u da kashi 35 cikin dari, Sall kuma yake da kashi 26 cikin dari na kuri'un da aka kada.
Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta sharhinta ne a game da takaddamar dake tsakanin jam'iyar dake mulki a Afirka ta kudu, wato ANC da shugaban reshen matasa na jam'iyar, Julius Malema, wanda bayan sabani na lokaci mai tsawo, aka kore shi daga wannan jam'iya saboda matakan sa na bata sunan jam'iyar. Jaridar ta ambaci wata sanarwa daga kwamitin ladabtarwa na ANC dake cewar wannan mataki an dauke shi ne saboda Malema yaki yarda da zargin cewar ya aikata ba daidai ba, a duka matakan da yake dauka na bata sunan jam'iyar tun daga watannin baya. Daga cikin laifukan da aka zargi Malema tattare dasu, har da fita fili yayi kiran kayar da gwamnatin makwanciyar kasar Botswana, ya kuma kara zafafa sukan sa kan shugaban kasa Jacob Zuma. To sai dai jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace koran Malema daga ANC ba zai zama karshen zamanin sa na siyasa ba, saboda yana da matukar farin jini tsakanin matasa, wadanda suke ganin sa a matsayin abin misali a jam'iyar ta ANC.
A makon jiya, aka gudanar da taron kasashe sittin da masu ruwa da tsaki a kokarin ganin an sami zaman lafiya a Somalia. Wannan taro da kuma halin da kasar ta yankin kahon Afirka take ciki, ya baiwa jaridar Die Tageszeitung damar sharhi game da halin da yan gudun hijira suke ciki a sansani mafi girma a duniya dake Dadaab a arewacin Kenya. Jaridar tace kungiyar likitocin duniya ta baiyana matukar damuwa a game da halin da sansanin yake ciki, musamman game da kara munin yanayin zama a cikin sa Ita ma hukumar yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya tayi gargadin cewar yan gudun hijira dubu 463 dake zaune a sansanin na Dadaab nan gaba kadan kasancewra su a can zai gagara, sai fa idan an dauki matakan gagawa na gyara. Yayin da aka maida hankali ga ita kanta Somalia, ba kuma za'a iya kau da idanu game da matsayin dimbin yan gudun hijira da suka tsare daga kasar suke zaune a sansanoni a ketare ba.
Da wannan sharhi na jaridar Die Tageszeitung muka zo karshen shirin na Afrika a jaridun Jamus na wannan mako.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Muhammad Nasiru Awal