Gabas Ta Tsakiya: Bukukuwan babbar sallah
May 27, 2026
A Saudiyya an gudanar da aikin Hajji da Sallar Idi cikin tsauraran matakan tsaro, musamman saboda tashin hankali a yankin da rikicin Iran da kawayenta. Sama da mutane miliyan daya ne suka halarci Hajjin bana, ciki har da dubban Iraniyawa da Irakawa.
Fargabar tsaro ta rage armashi
A Iran, an gudanar da sallar cikin yanayi na ibada da addu'o’in zaman lafiya. Masallatai da filayen Idi sun cika da masu ibada musamman a Tehran da Mashhad, yayin da gwamnati ta mayar da hankali kan tsaro saboda yanayin rikicin yanki. Iyalai sun gudanar da layya tare da rabon nama ga mabukata, kamar yadda al'ada ta tanada.
A Turkiyya, dubban mutane sun gudanar da Sallar Idi a manyan masallatai irin su Blue Mosque da Hagia Sophia a Istanbul. Hukumomi sun samar da hutun Sallah, yayin da jama'a suka mayar da hankali kan ziyartar iyalai da kuma yawon bude ido saboda lokacin hutun bazara.
Siyasar cikin gida ta takaa rawa
A Iraki, bukukuwan sun gudana cikin yanayi dabam-dabam. A Baghdad da Najaf da Erbil, an gudanar da Sallar Idi tare da rabon kayan abinci ga marasa karfi. Sai dai matsalolin tsaro da siyasar cikin gida, sun rage armashin shagulgula a wasu yankuna. Kurdawa da Larabawa, sun gudanar da bukukuwan karkashin al'adunsu na musamman.
A Yemen kuwa bukukuwan Sallar Layya sun zo ne cikin mawuyacin hali, saboda yaki da matsalar jin-kai. Duk da karancin abinci da matsalolin tsaro, al'umma sun gudanar da Sallar Idi tare da kokarin faranta ran yara da taimakawa mabukata. A biranen Sana'a da Hodeidah an ga mutane suna taruwa, domin addu'o'in zaman lafiya.
Wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar