1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukukuwan karrama Nelson Mandela

December 10, 2013

Dubban mutane ne suka taru a Afirka ta Kudu suna juyayin mutuwar Nelson Mandela a zaman adduo'in da gwamnatin ƙasar ta shirya dan tunawa da gwarzon.

Barack Obama Graca Machel
Hoto: ALEXANDER JOE/AFP/Getty Images

Al'ummar Afirka ta Kudun baki ɗaya ba tare da la'akari ba da launin fata, ko addini ko kuma jinsi ba, suka haɗu wajen karrama wannan mutumin wanda ya sadaukar da rayuwarsa dan ganin 'yan ƙasar sun yi rayuwa cikin 'yanci da walwala. Yanayin da ya kasance ke nan yau da rana a wajen adduo'in da aka shirya. Janet Völkel wata mai shekaru 51 na haihuwa kuma farar fatar Afirka ta Kudun, na ɗaya daga cikin ɗarurruwan jama'ar da suka halarci wannan buki da ya gudana a filin wasannin Ellis Park, ta shafe sao'i biyu tana zaune cikin ruwan saman da ya yi ta kwarara tana ƙoƙarin rufe kanta da ƙyalen tutar ƙasar.

Janet Völkel ta ce bayan da ta sami labarin rasuwar Mandela ranar jumma'ar da ta gabata, ta kira ɗaya daga cikin ƙawayenta domin sanar da ita kuma saboda irin nauyin da labarin ya yi a zuciyarta sai da ta fashe da kuka tana cewar na san da cewa zai rasu, kuma a zahiri labarin ya jefa ni cikin wani yanayi.

Obama yana gaisawa da shugaban Kuba Raul CastroHoto: Getty Images

Yadda mutane suka yi yawa wajen wannan buki wanda aka watsa shi kai tsaye a gidajen talabijin na duk duniya ya sanya ƙarancin kujerun zama, a filin wasannin na Soweto an sami halartar kusan mutane dubu 95. Tun asuban farko jama'a suka fara tururruwa zuwa wannan wuri, kuma kasancewar shugabannin gwamnatociu fiye 91 wani abu ne da ba'a taɓa gani ba, jaddawalin sunayen shugabanin bai tsaya daga Shugaba Barack Obama na Amirka zuwa Hamid Karzai na Afghanistan ba, har ma da 'yan siyasan da ba a cika ambatan sunayensu ba a ƙasashen yamma, waɗanda kuma suka zauna a kan teburin manyan baƙin waɗanda kuma suka haɗa har da shugaban ƙasar Kyuba, Raoul Castro da kuma shugaban ƙasar Zimbabwe Robert Mugabe wanda jama'a suka yi ta ihu suna jinjina masa.

Iyalan Mandelan ma ba a bar su a baya ba, inda dukkansu suka sami halarta, jama'a sun nuna farin ciki sosai da tsohuwar matarsa Winnie Mandela ta shigo cikin filin wasan, amma kuma ba su nuna irin wannan farin cikin sosai ba lokacin da matarsa ta yanzu Graca Machel ta shigo ba.

Jawaban da aka gabatar na cike da yabo wa Nelson Mandela, "Makoki ne ake yi kan babban rashi da kuma farin ciki kan rayuwa ciki da gwagwarmaya", kwatancin da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya yi ke nan a jawabinsa yana la'akari da rawar da mamacin ya taka a ƙasar da ake wa laƙabi da Rainbow nation a turance.

MahalartaHoto: Reuters

"ya sadaukar da komai kuma a shirye yake ya bada duk abubuwan da yake da shi domin samar da 'yan cin walwala da daidaitawa, da demokraɗiyya da kuma adalci"

Da ya fara waƙoƙin yabon Mandela shugaba Barack Obama na Amirka ya kwatanta shi a matsayin wani labari wanda ba za'a manta ba kuma ya bayyana abubuwan mamakin da yayi inda a cewarsa ya kasance gwarzon walwala da zaman lafiya

Shugaba Jacob ZumaHoto: Reuters

"Ya faɗa mana abin da za a iya aikata wa, ba a shafukan litattafan tarihi kaɗai ba, har ma da rayuwar da mu kanmu muke yi"

Waɗanda suka halarci wanann taro na adduo'i dai sun ce suna makoki ne kuma suna godiya kuma duk shugabanin da suka halarci wannan taro mutane ne da a buɗe suke nuna goyon bayansu da gwagwarmayar da Mandela yayi a tsawon rayuwarsa.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Abdourahamane Hassane