Yadda babbar Salla ta gudana a sassan duniya
June 28, 2023Lokacin da al'umomin kasashen Larabawa ke bin sahun sauran Musulman duniya wajen gudanar da bukukuwan Sallar layya, tashe tashen hankula da tsadar ragunan layyar, na rage karsashi da armashin bukukuwan sallar. Farawa daga birnin Makkatul Munawwarah, yadda maniyata ke karkare aikinsu na Hajji don su zama cikakkun Alhazai, yadda a ranar ta yau za su gudanar da jifan shedan da yanka ragon fansa da yin aski ko sosoye, gami da yin sassarfa tsakanin Safa da Marwa, kafin yin dawafin Ifadha da ke kawo karshen manyan rukunan aikin Hajji.
Karin Bayani: Bikin Sallah Karama bayan kammala azumi
Wasu daga cikin Alhazan da suka gama wadannan rukunan baki daya, wadanda ba a shardanta sai an gudanar da su a jere ba, sun bayyana murnarsu da irin wannan gamo da katar din da suka yi, cikinsu har da Haj Ibrahim Richman, wani tsohon Pada dan kasar Afirka ta Kudu da ya Musulunta watanni uku da suka gabata. A masallacin Al-Aqsa duk da matakan da jami'an tsaron Isra'ila sukai ta sanyawa masallata, masallacin ya yi cikar kwari da masallata,yadda limamain da ya jagoranci sallar Idi,yayi addu,ar nemawa kasar Falalsdinu dama sauran wadanda ake danne da su a duniya 'yanci.
A kasar Sudan kuwa, wacca duk da bayyana tsagaita wutar radin kai da bangarori masu fada da juna suka yi, a safiyar yau sallah, akai ta jin amon barin wuta a biranan Khartoum da Bahry da Umdurman, limamai a massalatai ne ke tayin adu'oin Allah kawo karshen yakin da ke neman wargaza kasar, a yayin da tsada da rashin kudi suka hana mutane layya, kamar yadda wani mai sayar da ragunan ya tabbatar.