Bukukuwan sallar Maulidi a kasashen Musulmi
December 23, 2015Al,ummar Musulmi a kasashen larabawa na bukuwan Maulidi da aka saba yi duk shekara ,don tunawa da ranar da aka haifi fiyeyyen halitta, Annabi Muhammadu S.AW.
Illahirin kasashen na Larabawa dai yau ranar hutu ce, don tunawa da ranar da aka haifi Ma,aiki S.A.W, kan banda kasar Saudiyya wacca duk da tana haramta bukukuwan na Maulidi, ta kunna koriyar wuta kan kubbar dake Raular Ma'aiki S.A.W hasken wutar da ya luluka ya haskaka sararin samaniya.
Ana gabatar da tarihin Ma'aiki a tarukan maulidi
A kasar Masar kuwa yadda ake rarraba alawa da kayan makulashe gida-gida, dubbun mutanene su ka yi gangami a hubbaren Sayyidina Husaini Jikan Ma,aiki S.A.W.
Sheik Umar Hasheem, shugaban shehunan darika a kasar ta Masar ya fadi dalilin shirya wannan gangami na Maulidi:
"Ya Babbar Rahamar da Ubangiji ya yi mana baiwa da ita.Ya Kai da ka zama babbar ni'imar Ubangiji da ya yi mana kyautarta. Ba munt aru muna tunawa da ranar haifuwarka bane don mun manta da kai, Sam har abada, mun dai taru ne don nuna godiya ga mai duka, da kuma tuna wa rafkanannu tarin daraja da girman da Allah ya baka. Domin kullum muna ambatanka, cikin salla da salatin da muke ma a kowane lokaci."
Sha'irai na gabatar da kasidun yabon Annabi a tarukan Maulidi
A Daular Larabawa kuwa, hakimin masarautar Dubai ya rarraba kyaututtuka ga masu kasidun da suka kambama Ma'aiki S.A.W
Hakama bukukuwan suka kasasance a kasashen Tunusiya da Libiya da Aljeria. A Kasar Maroko kuwa, yadda sarkin kasar Muhammad Sadis da kansa ya shirya hawan daba masu yaban Ma'aiki ne sukai tayin shauqi.
A kasar Iraki kuwa, yadda dubban masoya Ma'aiki suka cika makil a garuruwan Karbala da Khazimiyya da A'azamiyyah mutane sun yi ta yi wa kasashensu dama al,ummar musulmi addu'ar zaman lafiya da kwanciyar hankali da kyakyawar cikawa.
"Wallahi gashi munzo wannan bikin maulidi cikin kwalliya da murna da farin ciki da nuna kauna ga Ma'aiki S.A.W. Muna fata Allah ba wa kasarmu Iraqi dama sauran kasashen musulmi zaman lafiya ya kuma maimaitamana"