1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Afirka ta Kudu: Sabon nau'in corona

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 25, 2021

Masana kimiyya a Afirka ta Kudu, sun bayyana gano wani sabon nau'i na kwayar cutar coronavirus da ta addabi duniya a kasar.

Illustration eine Coronavirus-Mutation
A nahiyar Afirka, coronavirus tafi yawa a Afirka ta KuduHoto: DesignIt/Zoonar/picture alliance

A cewar masana kimiyyar na Afirka ta Kudu, sabon nau'in na yaduwa cikin gaggawa kuma mutane da dama sun kamu. Adadin wadanda ke kamuwa da annobar COVID-19 din a kasar da ke neman zama cibiyar corona a nahiyar Afirka, ya karu tun daga farkon wannan wata na Nuwamba da muke ciki. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta bayyana cewa tana bin rahoton bullar sabon nau'in na Afirka ta Kudu sau da kafa. Rahotanni sun nunar da cewa an samu sabon nau'in a kasar Botswana da yankin Hong Kong, a jikin wasu fasinjoji da suka fito daga Afirka ta Kudun.