Bayern Munich ta kara zama zakara
June 29, 2020A ranar Asabar aka kammala kakar wasannin kwallon kafa a Jamus duk da kalubalen coronavirus da ta fuskanta, inda mako na 34 ya zame wa wasu kungiyoyi na cikon sunna saboda sun rika sun samma makomarsu.
Hasali ma duk da cewa wasan ba shi da wani tasiri a gareta, amma dai Bayern Munich ta lallasa Wolfsburg da ci 4-0, lamarin da ya daukaka matsayinta na zakaran da allah ya nufa da cara a karo na takwas a jere a bundesliga da maki 89. Wannan ya na nufin cewa sau 30 ke nan kungiyar da ke da mazuninta a kudancin Jamus ta lashe kambun zakarar kwallon kafar kasar cikin tarihi.
Hasalima dai ta zama mazari wanda ba wanda ya san gabanta saboda ita Yaya Babba ce ta zo a sahun farko na zura kwallaye a ragar abokan karawa inda ta zura 100, sannan ta yi takwarorinta zarra a karancin kwallaye 32 kacal da a zura mata. Bugu da kari ma dai, dan wasan Bayern Munich wato Robert Lewandownski ne ya kasance dan kwallo da ya fi zuwa kwallo a bana, inda ya tashi da 34.
Baya ga ita Bayern Munich, ita ma yaya karama Borussia Dortmund ta cancanci wakiltar Jamus a gasar zakarun Turai kasance ita ce ke da matsaqyi na biyu da maki 69 duk kuwa da shan duka tamkar kuran roko a hannu Hoffenheim ci hudu da nema. Sai dai Lucien Favre, mai horas da Borussia Dortmund ya ce wannan rashin nasarar bai dakushe burin da suka sa a gaba.
"Mun cimma burinmu tun sati daya da ya wuce. Kuma ba mu yi wasa mai kyau wajen kwace kwallo ba kuma ba mu matsa wa abokan hamayyar lamba yadda ya dace ba. A gaskiya ba mu yi rawar gani a wasan karshe ba. Dan kwallo daya bai yi wasa yadda ya kamata ba kuma ya dagula komai."
Ita kuwa RB Leipzig ta gama kakar ne a matsayi na uku da maki 66 bayan da ta doke Ausburg da ci buyu da daya a karshen mako, lamarin da ya sa kungiya ta uku da za ta wakilci jamus a gasar zakarun Turai, yayin da Mönchengladbach za ta kasance ta hudu bayan da ta doke Hertha Berlin da ci 2-1.
Sai dai a kasan teburin Bundesliga an fuskanci ba zata da Werder Bremen wacce aka yi hasashen cewa za ta koma matsayin Bundesliga na biyu, amma kuma maimakon haka ta cire wa kanta kitse a wuta ta hanyar doke Fc köln ci 61, godiya ta tabbata ga Yuya Osako, dan wasan da ya zura biyu daga cikin kwallayen.
A takaice dai, Sai Bremen ta yi wasa sanin mako da Heidenheim a ranar Alhamis ne za ta san ko za ta ci gaba da zama a babban lig koko a'a. Amma bai hana Florian Kohfeldt, mai horas da Werder Bremen nuna alhini game da komabaya da düsseldorf ta samu kanta a ciki ba.
"A wannan lokacin ina juyayin abin da ya samu Düsseldorf, wanda ta taka leda sosai bayan da aka dawo hutun rabin lokaci, sannan ta saba wasa mai yawa, amma ko yaushe tana samun kanta cikin mawuyacin hali. Ko da shi ke ina murnar nasarar da muka samu, amma ina lahinin abin da ya samu 'yan Dusseldorf.2.
Kungiyoyi biyu da suka haye babban lig din kwallon kafar Jamus wato Paderborn da Düsseldorf a bana sun suka sake tattara na su ya nasu suka koma lig na biyu. Yayin da Arminia Bielefeld da Stuttgart suka cancanci shiga babban lig din Jamus.