Bundesliga Radio kai-tsaye
August 26, 2016Tun daga ranar 27 ga watan Augustan shekara ta 2016 muka fara gabatar da wasannin Bundesliga kai-tsaye ta harsunan Hausa da Suwahili, sannan daga bisani sassan harsunan Faransanci da na al'ummar Portugal suka shiga sahu. A kakar wasanni ta 2019/20 Sashen Ingilishi ya shiga jerin masu kawo muku wannan sharhi na gasar Bundesliga.
Shekarar ta 2019 ta kasance kakar wasanni ta hudu da muke gabatar da bayanai kan Bundesliga. A cewar tsohon abokin aikinmu da ke zama kwararren mai gabatar da sharhi kan harkokin wasannin motsa jiki Umaru Aliyu "wannan tamkar mafarki ne da ya zama zahiri."
Gasar wasannin Bundesliga kai-tsaye
Kai tsaye kamar yadda muka saba, ma'aikatanmu ke gabatar muku da sharhin wasu daga cikin wasannin da suka fi kayatarwa tare da hadin kan kwararru a fannin wasannin kwallon kafa na tashar DW.
A cewar shugaban Sashen Afirka na DW Claus Stäcker "Afirka nahiya ce da al'ummarta ke kaunar wasannin kwallon kafa. Kuma masoya kwallon kafar sun san sunayen kusan kowa da ke buga kwallo a tawagar kwallon kafar Jamus da ta sha zama zakara a harkokin wasanni a duniya."
Ma'abota wasannin Bundesliga da dama a nahiyar Afirka ke ba da gudunmawa wajen tallata gasar ta Bundesliga a kowace shekara inda alal misali a birnin Kadunan Najeriya Mohamed Mohamed na tashar Freedom Radio Kaduna, ke shirya gasar Bundesliga a tsakanin kungiyoyin birnin na Kaduna tare da rarraba masu kyaututtuka na Jersey na kungiyoyi dabam-dabam da ke bugawa a rukunin Bundesliga babba irin su Bayern Munich da Dortmund.
Wasannin Bundesliga a ranaikun Asabar
Za ku iya sauraron shirin na wasannin Bundesligar kai-tsaye da misalin karfe biyu da minti 25 agogon Najeriya, Nijar Kamaru da Chadi, wato karfe daya da minti 25 agogon GMT da Ghana, ta hanyar gajeren zango kan mitoci 19 kilohaz 15195 kilohaz 15350.
Za ku iya sauraronmu kai tsaye ta shafinmu na intanet da na Facebook na DW Hausa lokacin da ake wasan ko kuma a tashoshi abokanan huldar DW da ke a yankunanku a wadannan kasashe:
Najeriya:
BRC - Bauchi
Caliphate - FM Sokoto
Dandal Kura - Maiduguri
Freedom Radio - Kano, Dutse, Kaduna
Liberty FM - Kaduna, Abuja
Progress Radio - Gombe
Radio Gotel - Yola
Rima FM 97.1 - Sokoto
Platinum FM - Keffi
Prestige FM - Minna
Unity FM - Jos
Nijar:
Alternative - Diffa
Anfani - Niamey, Konni, Maradi, Diffa, Zinder
Dallol - Balleyara, Dogondoutchi, Matankari, Tibiri
Damergou- Tanout
Dileram - N'Guigmi
Fara'a - Djoundjou, Dosso, Gaya
Gagaraou - Birnin Kazoé
Gaskia - Zinder
Haddin-Kay - Aguié, Dakoro, Magaria, Tagriss
Kaocen - Arlit
Niyya - Konni
Nomade - Agadez
Rounkondoum - Doumega
Saraounia - Konni, Madaoua, Maradi, Tahoua
Shukurah - Matameye, Zinder
Tambara - FM Tahoua
Tarmamoua - Tessaoua
Té Bon Sé - Tillabéri
Ghana:
Zuria FM – Kumasi
Senegal:
Radio Dunyaa FM – Tamba