Najeriya: Bunkasa kasa ko cinye dukiyar kasa?
September 10, 2025
Duk da cewar dai ba a kai ga sanya ranar aiwatar da karin harajin man fetur din ba, gwamnatin kasar ta ce sabon harajin ya zama wajibi a koakarin da take na inganta al'amura. Kungiyar TUC ta manyan ma'aikatan Najeriyar dai ta ce, ta bai wa gwamnati tsawon mako biyu ko dai ta manta da harajin ko kuma ta daka wani yaji irin na baba ta gani. Duk da cewar dai har yanzu yan kasar na ji a tsakar ka bisa zare tallafin man fetur, daga dukkan alamu Abujar na shirin dora wa bisa wani sabon harajin man fetur.
Ina makomar barazanar kungiyar kodago?
Masu mulkin kasar dai na fatan karbar karin kaso biyar cikin 100 a kan kowace litar man, a matsayin harajin da masu mulkin ke fatan ka iya kai wa ga mayar da tsohuwa yarinya cikin batun hanyoyi a kasar. Kuma daga dukkan alamu wata barazanar masu kodagon Najeriyar dai ta gaza shawo kan mahukuntan, domin su manta da harajin da ke neman yamutsa hazo cikin kasar a halin yanzu. Abujar da aka ce bai dace ta kirkiro da sabon harajin ba, ta sa kafa ta shure adawa ga kokarin dakile aiwatar da shi.
Karin Bayani: CBN ya kara harajin cire kudi ATM a Najeriya
Taiwo Ayodele dai na zaman shugaban kwamitin gwamnatin kasar, wanda ke kula da gyaran fuskar tsarin harajin Tarayyar Najeriyar. "Wannan haraji abu ne da ake a ko'ina a duniya, akwai shi a kasashe fiye da 150 na duniya. Wasunmu na yin tafiya zuwa waje kuma muna fadin hanyoyi sun fi kyau a Ghana ko a Kenya ko a Birtaniya, amma kuma babu wata kasa da ke yin hanyoyi da kudin da take bugawa."
Karin haraji hanyar samar da kayan more rayuwa?
Ayodele ya kara da cewa: "A karshe kudin na zuwa ne daga wasu wurare, sama da kasashe 150 na da harajin da su kan ware domin hanyoyi. Idan hanyoyi na da kyau,to zirga-zirga za ta zamo mai sauri mara hatsari kuma kishe kudin gyaran motoci zai ragu. A kasar Afirka ta Kudu, ana biyan abun da ya kai kusan kaso 30 cikin 100 na farashin man fetur a cikin harajin hanyar."
A cewarsa: "A Ghana, akwai haraji iri-iri har guda shida a harkar fetur. Ba ina fadin ayi haka a Najeriya a yanzu ba, amma lokaci zai zo na yin hakan. Kila a lokacin da darajar Naira ta daga da kaso biyar ko 10, in an yi haka ba ma za mu ankara ba." Koma ya zuwa ina Abujar ke fatan kai wa a kokarin birge ma su kodagon da ma jama'ar cikin gari bisa sabon harajin, daga dukkan alamu suna da sauran tafiya cikin hanyar da ke da tsidau da kaya.
Gyara ko yin wasoso da dukiyar kasa?
Kungiyar TUC ta masu kodagon kasar dai ta ce a kai ga kasuwa a tunanin harajin, walau a yau ko gobe a tunanin Dakta Abbayo Nuhu da ke zaman sakataren kungiyar manyan ma'aikatan kasar TUC. Wa-kaci ka-tashi da dukiya ta 'yan kasa ko kuma neman mafita a hanyoyin da ke ta kara lalalcewa, a baya dai wani asusu da gwamnatin mulkin sojan kasar ta kirkiro daga rara ta karin farashin man tai nasarar taka rawar da ke da girman gaske cikin batun hanyoyin da kila ma ragowa na ababen more rayuwa.
Karin Bayani: Shirin sabuwar dokar haraji a Najeriya
To sai dai kuma ya zuwa yanzun a tunanin Dakta Isa Abdullahi da ke zaman kwarrare a fannin tattalin arziki, yanayin da ke cikin kasar ya sauya da ba ya bukatar matsi ga rayuwar al'umma. A shekara ta 2004 ne tsohuwar gwamnatin Chief Olusegun Obasanjo ta rushe daukacin shingayen hanyoyi na kasar bisa zargin wasoso da dukiyar al'umma, abun kuma da ya kai ga lalacewar kaso kusan 70 cikin 100 na hanyoyin da ke a Tarayyar Najeriyar a halin yanzu.