1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bunkasa kasuwanci tsakanin Amirka da Afirka

August 7, 2014

Karfafa hulda da zuba jari da kuma maganar cinikayya da tsaro wadannan su ne muhimman abubuwan da aka cimma a taron Amirka da kasashen Afirka.

USA-Afrika-Gipfel in Washington
Hoto: Reuters

Shugaba Barack Obama na ganin tabbas ya samu nasara a karshen taron, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu a yunukurinsa na takawa China birki, wacce ke zama jigo kana kuma kan gaba wajen huldar cinikayya da Afirka.

Amirka dai ta yi alkawarin bada tallafi na kudade sama da biliyan 30 ga gamnatocin kasashen domin tada komadar tattalin arzikinsu, tare kuma da zuba jari mai yawa ta hanyar kamfanoni da masantu masu zaman kasansu. Har na kusan biliyan 14 ga nahiyar wacce ake hasashen cewar a shekara ta 2015 za ta samu ci gaba da kusan kashi biyar cikin 100.

Rchar Downie kwararra ne kan sha'anin tattalin arziki wanda ke zaune a birnin Washinton a cikin hirar da tashar DW ta yi da shi ya ce a kwai burga dai a cikin lamarin;

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar KeitaHoto: picture alliance / AP Photo

Ya ce" biliyan 33 a rubuce a bisa takarda a kwai dadin fadi kuma ko ba komai a kwai burga idan ka ajiye hankalinka ka duba za ka ga cewar yawan kudaden da zasu je ga kasashen Afirka inda har bada ma zasu zo ne daga bakin duniya da sauran hukumomin kudin makamantansu. Amma maganar zuba jari abu ne mai kyau kuma mai karfi wanda a ciki za a iya samun kamfanoni irinsu Coca Cola da sauransu, amma shi ma kamar ka dauki bokiti guda ne na ruwa ka watsa cikin teku me ka yi kenan".

A duk tsawon taron da aka yi shugaba Barack Obama ya sha wasa Afirkan tamkar watan sallah sha kallo saboda yadda ya ce nahiyar na zaman wata sabuwa mai samun ci-gaba da gaggawa domin samun sukunin cike ratan da kasarsa ke da shi a kan hulda kasuwanci baya kwarai ga nahiyar turai da kuma china.

Mawallafi: Abdourrahman Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar