1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Habasha ta dauki matakin karfafa tattalin arziki

Suleiman Babayo ATB
December 17, 2024

Firaminista Abiy Ahmed na Habasha ya kara bude hanyoyin zuwa jari a kasar wajen amincewa da bude rassan manyan bankuna a kasar, domin karfafa tattalin arziki.

Firaminista Abiy Ahmed na kasar Habasha
Firaminista Abiy Ahmed na kasar HabashaHoto: Prosperity Party -Ethiopia’s ruling party

Majalisar dokokin kasar Habasha ta amince da kudirin dokar bude wani bangare na bankunan kasashe ketere a cikin kasar. Tun shekara ta 2018 lokacin da Firaminista Abiy Ahmed ya dauki madafun iko ya kokarin bude harkokin tattalin arzikin kasar da gwamnatin take rike da komai, domin samun masu zuba jari daga kasashe ketere da kara karfafa tattalin arzikin kasar. Karkashin sabuwar dokar kamfanonin kasashen ketere suna iya mallakar jari kaso 49 cikin 100.

Karin Bayani: Habasha: Shekaru 50 da kisan Haile Selassie

Kasar ta Habasha mai mutane milyan 120 take matsayi na biyu wajen yawan mutane a nahiyar Afirka kuma ta kasance mai samun bunkasa tattalin arziki cikin hanzari musamman daga shekara ta 2004 zuwa 2019 inda kasar take samun bunkasa na kaso 10 cikin 100 duk shekara. Amma yanzu kasar ta samu kanta a rikicin cikin gida.