1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Inganta tsaron Jamus

Suleiman Babayo ZUD
July 1, 2024

Ministar harkokin kasashen waje ta Jamus Annalena Baerbock ta nunar da cewa, ya zama wajibi kasar ta ci gaba da bunkasa fannin tsaro.

Ministar harkokin kasashen waje ta Jamus Annalena Baerbock
Ministar harkokin kasashen waje ta Jamus Annalena BaerbockHoto: Kira Hofmann/photothek/IMAGO

Kalaman na Baerbock na zuwa ne, duk da matsin lambar da mahukuntan na Berlin ke fuskanta kan su rage kason da ake warewa bangaren a daidai lokacin da suke fuskantar gagarumin kalubale a tattaunawar da suke kan kasafin kudin shekara ta 2025 da ke tafe. Da ma dai ministan kudin na Jamus, Christian Lindner na jam'iyyar (FDP) ta masu ra'ayin jari hujja ya bukaci gwamnatin hadakar ta Jamus, kan ta kaucewa duk wani nakasu a fannin kasafin kudin musamman ma ciyo bashi.

Karin Bayani: Jamus: Tantance masu neman mafaka a wata kasa

Sai dai Ministar harkokin kasashen wajen ta Jamus Annalena Baerbock da ta fito daga jam'iyyar The Greens ta masu rajin kare muhalli ta ce ya zama wajibi mahukuntan birnin Berlin su zama abin koyi a tsakanin kasashen Turai, musamman yadda Turan ke fuskantar gagarumin kalubalen tsaro ko da kuwa ta hanyar ciyo bashi ne.