Bunkasar tattalin arzikin Spain bayan tsawon shekaru
November 20, 2025
Farfadowar kasar Spain bayan annobar Corona na tafiya cikin hanzari. Hakan kuwa ya samu ne sakamakon bunkasar gine-gine da habakar yan yawon bude da fannin nishadi. Kama daga wuraren da ake gine-gine a Madrid har zuwa otel otel na wurin shakatawa da ke bakin kogi a Marbella, ma'aikata yan kodago daga kasashen waje na cike muhimman guraben kodago yayin da 'yan kasar suka karkata akalarsu ga manyan ayyuka da ke bayar da kudi masu yawa kuma mara wahala.
Da 'yan cirani fiye da 600,000 da suka isa kasar cikin shekaru biyu da kuma yan yawon bude ido miliyan 20 da ke kai ziyara, habakar tattalin arzikin kasar ya fi na galibin kasashen Turai. Sai dai kuma ayar tambayar ita ce, zuwa tsawon wane lokaci zai dore da kuma makomar kananan ayyuka da ke bukatar kwararru.
Yayin da ake kara samun cigaban na'urori masu sarrafa kansu kamar Andalusia na kara jan hankalin 'yan baiwa daga sassan duniya.
Bunkasar gine-gine a wurin shakatawa na bakin ruwa da kuma birane na habaka tattalin arzikin Spain. Sai dai duk sun dogara ne a kan ma'aikata 'yan kasashen waje, a cewar Patricia Hernández Cobo shugabar kamfanin Vía Ágora F1.
"Hakikanin gaskiya su ne masalaha ga matsalar mu ta karancin ma'aikata"
Juan Miguel Marcos Manajan Otel ya ce "ba tare da taimakon ma'aikata 'yan cirani daga waje ba, da ba za mu iya karbar 'yan yawon bude ido da yawa ba.."
Kawo yanzu, yawancin yan cirani suna aiki ne a fannin kananan ayyuka da ba a bukatar kwarewa mai zurfi, to amma Spain na kara jan hankalin masu harkokin kasuwanci da kuma kwararru a wasu fannioni. Hatta birnin Andalusia da ya yi suna wajen yawon bude ido ya fara sauyawa. Misali wurin shakatawa na fasaha da ke Malaga, tun karshen korona mutane masu baiwar fasaha da manyan manajoji da suka goge a harkokin kasa da kasa suke ziyartar birnin.
Pablo Alifano Managing Daraktan kamfanin Talan a Spain da Poland ya ce "mun dauki ma'aikata daga kasashe fiye da 28. Mun zabi Malaga saboda ingancin rayuwarsa. Yanayi da abinci da mutanen da ma zamantakewar tsirrai da hallitu suna jawo mutane yan baiwa su zo nan"
Zuwa nan gaba nasarar da Spain ke samu na iya zama kalubale. Idan tattalin arzikin kasar ya yi kasa, ma'aikata masu karancin kwarewa sune na farko da za su fara rasa ayyukansu