Bunkasar wasanni a shekaru 50 da kafa jihar Bauchi
February 5, 2026
Tun a farkon shekarun 1990 ne Bauchi ta fara shiga sahun jihohin da suka karbi bakuncin manyan gasanni a matakin kasa, inda ta fara da bikin baje kolin wasanni a 1991 na kasa ba ki daya ,da ke hada dukkanin jihohin kasar a wasanni daban-daban.
Nasarar karbar bakuncin ba tare da samun matsala ba, ya sa ma'aikatar wasanni ta Najeriya sake kawo gasar a karo na biyu a shekarar 2000. Sani Ahmad Toro, da ya kasance sakataren hukumar kwallon kafar Najeriya a shekarun 1990 ne ya jagoranci masu buga takardun neman jihar shekaru hamsin da suka gabata.
Karin bayani: Ahmed Musa zai iya kawo sauyi a Kano Pillars?
A shekarar 1999 ne jihar Bauchi ta fara karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya ta matasa, wanda a lokacin ne fitaccen dan wasan Brazil Gucho Ronaldinho ya fafata wasa a filin wasa na Sir. Abubakar Tafawa Balewa.
Sannan bayan shekaru 10 cif a shekarar 2009. jihar Bauchin ta sake karbar bakuncin gasar cin kofin duniyar ta 'yan kasa da shekaru 17. Sai dai bayan shekaru 17, jihar ba ta sake samun dama irin na baya ba.
A bangaren matasa ma, gasar 'yan kasa da shekara 17 ne ke ransu saboda sun shaidar da ita. Ko da yake tarihin da jihar Bauchi ta kafa a baya na da matukar tasiri a wajensu, kamar yadda Imrana Yakubu Galaje, ya bayyana duk da cewa a yanzu akwai tarin matsaloli.
Karin bayani: 'Yan matan Najeriya sun taka rawar gani
A yanzu haka, filin wasa na Sir. Abubakar Tafawa Balewa na bukatar dauki kafin nan gaba ya kai matsayin sake karbar bakuncin wata gasa ta duniya.