Burin kananan hukumomin Najeriya bai cika ba
July 11, 2025
A Najeriya an shiga takun saka dangane da gaza aiwatar da hukuncin kotun koli da ya bai wa kananan hukumomi cikakken gashin kansu, amma shekara guda babu labari, abin da ya sanya kungiyoyin ma'aikata kananan hukumomi nuna yar yatsa a kan lamarin.
Shekara guda ke nan cur da kotun kolin Najeriyar ta yanke wannan hukunci da ya haifar da ɗoki a tsakanin ma'aikatan kananan hukumomi 774 na Najeriyar, sai dai kuma shiru kake ji kamar an shuka dusa,.
Har yanzu babu wata karamar hukuma a kasar ta Najeriya da aka fara bai wa kudin nata kai tsaye, har yanzu gwamnoni ke karba kudadden. Kuma wannan ya harzuka wasu kungiyoyin farar hula da suka fara nuna 'yar yatsa kan cewa an fa kure hakurinsu.
Ta dai kai ga kungiyar kananan hukumomi sake daukar matakin shari'a a kan wannan lamari na bai wa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu ta hanyar ba su kudadensu kai tsaye daga mataki na kasa
Tun farko dai an fara da samun cikas a kan aiwatar da hukuncin inda aka fara da ɗaga kafa na watanni uku ga gwamnoni, sannan gwamnatin Najeriyar ta kafa kwamiti mai mutane 10 domin duba aiwatar da hukunci.
A yayin da ake wannan tirka-tirka inda gwamnonin ake nuna 'yar yatsa wadanda suka matse kanana hukumomin, ana ganin gaza bai wa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye babban koma baya ne da ke rusa daukacin matakin mulki na uku a tsarin dimukurdiyyar Najeriyar.